Home Labarai Shugaba Tinubu ya nada shugabannin asusun kula da manyan makarantun gaba da sakandire

Shugaba Tinubu ya nada shugabannin asusun kula da manyan makarantun gaba da sakandire

by masta

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin shugaba da membobin gudanarwa na asusun kula da manyan makarantu na ƙasa "Tertiary Education Trust Fund (TETFund)".

Mutanen da ya naɗa ɗin sun haɗa da:

(1) Alhaji Aminu Masari — Shugaba,

(2) Sanata Sani Ɗanladi — Memba

(3) Mista Sunday Adepoju — Memba

(4) Mista Nurudeen Adeyemi — Memba

(5) Madam Esther Onyinyechukwu Ukachukwu — Memba

(6) Malam Turaki Ibrahim — Memba

(7) Mista Aboh Eduyok — Memba.

Shugaba Tinubu ya hore su da su yi aiki cikin himma domin cimma manufofin da aka sanya a gaba na tallafawa ilimin gaba da sakandire da inganta shi.

Related Posts

Leave a Comment