Home Labarai Shugaban Ƙasa Tinubu ya Mika sakon Ta’aziyya ga al’ummar Iran da ma duniya Baki Daya kan wannan babban rashi da aka yi

Shugaban Ƙasa Tinubu ya Mika sakon Ta’aziyya ga al’ummar Iran da ma duniya Baki Daya kan wannan babban rashi da aka yi

by masta

*SHUGABAN TINUBU YA YI BAKIN CIKIN RASUWAR SHUGABAN IRAN IBRAHIM RAISI*

Shugaba Bola Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar Jamhuriyar Musulunci ta Iran bisa rasuwar shugaba Ebrahim Raisi tare da Ministan harkokin wajen kasar, Hossein Amir-Abdollahian, da wasu jami’ai gwamnatin kasar a wani hatsarin jirgin sama a jiya.

Shugaba Tinubu ya bayyana matukar bakin cikinsa kan wannan lamari mai tayar da hankali, inda ya bayyana shugaba Raisi a matsayin jagora mai kishin ci gaban kasar Iran.

Yayin da yake jajanta wa iyalan wadanda suka rasu a madadin gwamnati da al’ummar Najeriya, shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah Ya kara wa al’ummar Iran zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba.

Shugaban ya tabbatar wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran cewa ýan Najeriya na tare da su a wannan lokaci na ibtila’i

Related Posts

Leave a Comment