Home Labarai Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya Amince da Mayar da hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Kasa ( NACA) Zuwa ma’aikatar lafiya ta Tarayya.

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya Amince da Mayar da hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Kasa ( NACA) Zuwa ma’aikatar lafiya ta Tarayya.

by masta

Matakin ya biyo bayan kudirin shugaban na inganta fannin kiwon lafiya da kuma tabbatar da daukar matakai masu inganci don tinkarar kalubalen da ke tattare da cutar kanjamau a Najeriya.

Ana sa ran komawar hukumar ta NACA zuwa ma’aikatar lafiya da jin dadin jama’a ta tarayya za ta samar da hadin gwiwa tsakanin hukumar da sauran kungiyoyi masu alaka da lafiya, hakan zai taimaka wajen wadata ayyukan kiwon lafiya da inganta rayuwar al’ummar Najeriya baki daya.

A yayin da sabuwar gwamnati karkashin jagorancin shugaba Tinubu ke ci gaba da aiwatar da sauye-sauye a sassa daban-daban, ana kallon sauyin shekar hukumar ta NACA a matsayin wani DanBa na samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya a Najeriya

Related Posts

Leave a Comment