Home Labarai Gwamnatin jihar Katsina ta kulla yarjajjeniya da China

Gwamnatin jihar Katsina ta kulla yarjajjeniya da China

by masta

Gwamnatin Jihar Katsina ta Kulla Yarjejeniya da
China Energy and Engineering Company domin Inganta Harkar Ruwa a Fadin Jihar Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagoranchin Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ta sanya hannu akan yarjejeniya da Kamfanin China domin Inganta harkokin ruwan sha a Jihar Katsina. Sa hannun ya gudana a fadar Gidan Gwamnatin Jihar Katsina a ranar Laraba, 13 ga watan Maris 2024.

Shugaban Hukumar Samar da Ruwa (Katsina State Water Board) Injiniya Tukur Tinglin ne ya jagoranchi kulla yarjejeniyar a madadin Gwamnatin Jihar Katsina.

Muhimman ayyukan da za a gudanar a wannan yarjejeniya sun hada da inganta dam na gwaigwaye a Karamar Hukumar Funtua, inganta dam na Malumfashi, inganta dam na Mashi, inganta dam na Jibia tare da gina sabon Dam a Katsina.

Haka kuma, yarjejeniyar ta hada da gina sabuwar headquarter ta Hukumar Samar da Ruwan sha, samar da wuta mai amfani da hasken rana a dukkan tashoshin ruwa na fadin Jihar Katsina, samar da fasahar sanin zaizayewar ruwa (water leakages) tare da gina sabuwar tashar sarrafa bahaya don samar da ruwa da samar da BioGas (gas don dahuwa), da dudduga domin yin taki.

Gwaman Malam Dikko Radda ya bayyana jin dadin sa tare da ba kamfanin tabbacin cewa Gwamnatin sa a shirye take ta basu duk wata kulawa da goyon baya domin ganin an samu nasarar wannan yarjejeniya da a ka kulla.
Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar Katsina, Hon. Hamza Sulaiman Faskari yana daga cikin wadanda suka shaida wannan muhimmin zama.

Isah Miqdad,
SSA Digital Media to Katsina State Governor.
13/3/2024

Related Posts

Leave a Comment