Daga: Bashir Abdullahi El-bash
Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabar ƙungiyar makarantun kimiyya, ranar Alhamis a fadar shugaban ƙasa, Abuja.
Tinubu ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta kai wani mataki na cigaba wajen rungumar fasahohi da ƙirƙire-ƙirƙire na ƴan Najeriya waɗanda za su samar da masalaha a kowane fanni na rayuwa waɗanda suka haɗa da Noma, ƙirƙira, fasahar zamani da harkokin sadarwa da fannin ilimi.
"Ministan ilimi, ministan lafiya da walwalar al’umma, da ministan kasafi da tsare-tsare duk suna wannan waje. Duk wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati ya zama wajibi su zauna su tabbatar da cewa sakamakon binciken kimiyya ya zama hanyar da za ta jagoranci inganta fannoni daban-daban masu fa’ida. Lallai ka da mu yi ƙasa a gwiwa wajen amfani da sakamakon bincike". -Shugaban ƙasa.
A nata tsokacin shugabar ƙungiyar makarantun kimiyyar, Farfesa Ekanem Braide, ta gode wa shugaban ƙasar bisa goyon bayan da yake ba wa asusun gudanar da bincike na ƙasa, inda ta ƙara da cewa ba shakka hakan zai taimaka wajen magance matsalolin da ake fuskanta tare da taimaka ƴan ƙasar ta kowane fanni.


