Home Labarai SANATA ABDULAZIZ YARI YA BA WA SHUGABA TINUBU GUDUNMAWAR KAYAN ABINCI A RABAWA ƳAN NAJERIYA SAMA DA MUTUM MILIY AN BIYU

SANATA ABDULAZIZ YARI YA BA WA SHUGABA TINUBU GUDUNMAWAR KAYAN ABINCI A RABAWA ƳAN NAJERIYA SAMA DA MUTUM MILIY AN BIYU

by masta

Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar, ya ba da gudunmawar tirelolin shinkfa da ƙunshin kayayyakin masarufi waɗanda suka haɗa da shinkafa, mai, taliya, suga, makaroni, gishiri, da sauransu domin a rabawa talakawa masu ƙaramin ƙarfi su rage raɗaɗin halin tsadar rayuwa da ake ciki gami da samun abin shiga Ramadan ga waɗanda suke musulmai.

Babban mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin sadarwa, Malam Abdulaziz Abdulaziz ne ya jagoranci waɗanda suka wakilci Shugaba Tinubu domin shaida yadda ake rabon kayayyakin abincin a wuraren ajiya dake Abuja da Kano.

Hon Muhammad Garba Gololo wanda ya kasance wakilin Sanata Yari wajen miƙa kayan a Abuja ya bayyana cewa sun ba wa shugaba Tinubu wannan gudunmawa ne domin su tallafawa ƙoƙarin gwamnatinsa wajen ragewa al’ummar Najeriya raɗaɗin halin da suke Ciki.

Da yake jawabi a yayin duba rabon shinkafa daga rumbunan ajiya dake Kano, Dr Abubakar Nuhu Damburam, wanda ya wakilci Sanata Abdulaziz yari ya ce za a raba buhunan shinkafa dubu tamanin da hudu (84,000) ga mabuƙata ta hannun malaman addini, sarakuna da kuma sauran shugabannin al’umma.

Da yake maida jawabi, babban mai taimakawa shugaban ƙasa Tinubu kan harkokin sadarwa, Malam Abdulaziz Abdulaziz, ya yabawa Sanata yari bisa wannan ƙoƙari tare da kira ga sauran masu hali da su yi koyi da shi wajen tallafawa al’umma masu ƙaramin ƙarfi kamar yadda shugaban ƙasa ke kiraye-kirayen a yi hakan.

Related Posts

Leave a Comment