Maigirma Dan Majalissar Tarayya Mai Wakiltar Bichi kuma Shugaban Kwamitin Kasafi Na Majalissar Tarayya, Hon. Abubakar Kabir Abubakar ya kaddamar da rabon shinkafa don tallafawa Al’ummarsa bisa karatowar watan azumin Ramadan inda yau aka fara da Mazabun Yallami da Kwamarawa.
Maigirma Dan Majalissar yayi wannan tunani ne domin taimakawa Al’ummar karamar Hukumar Bichi saboda hali da ake ciki na matsin rayuwa inda duk mutum daya zai karbi buhun shinkafa (50kg).
A jawabinsa, Shugaban Ma’aikatan Dan Majalissar Tarayyar Hon. Sabo Iliyasu Saye wanda shine ya wakilci Maigirma Dan Majalissar Tarayya yayi kira ga Al’ummar da suka rabuta da wannan abinci da suyi amfani da shi yadda ya dace sannan kuma ya tabbatar da cewa Maigirma Dan Majalissar Tarayya a shirye yake ya cigaba da taimakawa Al’ummar Karamar Hukumar Bichi yadda ya kamata kamar yadda ya saba.
Taron ya samu halartar daukacin Ma’aikatan Maigirma Dan Majalissar Tarayya, shugabannin Jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Bichi da sauran Al’umma.
Jamilu Halliru Master,
Babban Darattan Yadda Labarai da Hudda da yan’jarida Na Hon Abubakar Kabir Abubakar Bichi (FoE)






