A wata sanarwa da ya fitar, Sarkin Kano na 14, kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Khalifa Muhammadu Sanusi II ya ce sauya shekar wasu sassan babban bankin kasa zuwa Legas mataki ne mai kyau
“Abinda na kudirci yi a raina shine zan mayar da bangaren FSS da akasarin ayyuka zuwa Legas ta yadda mataimakan gwamnonin biyu ko fiye da haka za su rika gudanar da ayyukansu daga can tare da dimbin ma’aikatansu
Sarki Sunusi ya yi watsi da masu adawa da manufar inda ya ke cewa "babu wani abin tayar da jijiyar wuya a a kai tunda dama can CBN na da ma’aikatan da ke kula da rassanta da ofisoshin kuɗi a duka jihohin Najeriya
"Mayar da ma’aikata zuwa ofishin Legas don inganta aiyuka da rage kashe kudi wani tsari ne da al’adar gudanar da aiyyuka ta gada"
In ji Sarki Sunusi II


