Home Labarai Za mu hukunta duk me rawanin da aka Samu Yana aikata barna a yankin masarautar Gaya.

Za mu hukunta duk me rawanin da aka Samu Yana aikata barna a yankin masarautar Gaya.

by masta

Daga Bello Usman
GTR HAUSA

Masarautar Gaya tayi alkawarin hukunta duk Mai Unguwar da aka samu ya aikata barna a yankinsa, ba tare da ya sanar wa jami’an tsaro ba.

Dakta Aliyu Ibrahim ya bayyana hakan ne, lokacin da ya karbi bakuncin kwamishinan ‘yan sandan Kano CP. Muhammad Usaini Gumel, a fadarsa dake Garin Gaya.

Kuma dai ziyarar kwamishinan ta zo ne, a sakamakon zaman sulhun da Sarkin ya jagoranta, dangane da fadan da ya afku a garin Kademi dake karamar hukumar Gaya a makon daya gabata.

Sarkin ya kara da cewa, zaman lafiya shine ginshikin ci-gaban kowacce al’umma, inda yaja hankalin ‘yan siyasa da su dinga sanya Mabiyansu kan hanyar da ta kamata, dan samun ingantacciyar al’umma.

Haka kuma Sarkin ya yaba wa Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Kano, a bisa Kokarinsa na dakile matsalar tsaro a fadin jihar.

A nasa jawabin Kwamishinan ‘Yan sandan jihar kano CP. Muhammad Usaini Gumel, yace sun kaiwa kwamishinan ziyarar ne domin neman tabarraki sarkin, dama kamo bakin zaren matsalar da ta faru a garin kademi, wadda ta kai har da zubar da jinin wasu Mutane.

Ya kuma godewa Sarkin, a bisa kiran Dagacin Kademi da Masu Unguwanni, Limamai da wadanda abun ya shafa, domin tabbatar da sulhu a tsakaninsu.

Taron sulhun ya sami halartar shugabannin kananan hukumomin Gaya, Gabasawa, Dawakin Kudu, Dagacin Kademi, dukkan masu unguwannin yankin, Limamai, dama sauran bangarorin da abin ya shafa.

Related Posts

Leave a Comment