Home Labarai GEMT. Mai martaba sarkin Gaya Alh (Dr) Aliyu Ibrahim ya kar6i bakuncin kungiyar stoffin dalibai ta Federal college of agriculture products hotoro Kano(Alumni), karka shin jagorancin Umar Muhammad Garba a yayin zaman fadar yau Litinin, sunzo fadar ne domin Neman Tabarraki da shawarwari.

GEMT. Mai martaba sarkin Gaya Alh (Dr) Aliyu Ibrahim ya kar6i bakuncin kungiyar stoffin dalibai ta Federal college of agriculture products hotoro Kano(Alumni), karka shin jagorancin Umar Muhammad Garba a yayin zaman fadar yau Litinin, sunzo fadar ne domin Neman Tabarraki da shawarwari.

by Muhsin Tasiu Yau

GEMT.

Mai martaba sarkin Gaya Alh (Dr) Aliyu Ibrahim ya kar6i bakuncin kungiyar stoffin dalibai ta Federal college of agriculture products hotoro Kano(Alumni), karka shin jagorancin Umar Muhammad Garba a yayin zaman fadar yau Litinin, sunzo fadar ne domin Neman Tabarraki da shawarwari.

A nasa jawabin Mai martaba sarki,ya Gode musu tare da Basu shawarar ci gaba da wayar da kan al’umma kan muhimmancin noma.

A wata takarda Me dauke da sa Hannun Comr. Ubaliyo Falalu Gaya Mashawarci ga Sarkin Gaya kan kafafen sada zumunta na zamani ya bayyana cewa,Har ila yau Hukumar kula da kiyaye hadura( federal road safety) reshen Masarautar Gaya sun kawo ziyara karka shin jagorancin DD Auta,inda suka zo domin Godiya ga Mai martaba sarki bisa irin Gudun muwa da suka samu da hadin kan Masarautar wajen Gudanar da aiki yadda ya kamata,da shaidawa Mai martaba sarki cewa lokacin wa’adin aikin kwamandan zai cika farkon sabuwar shekarar January.

Cikin jawabin Sarkin Gaya ya Godewa musu tare da tabbatarwa kwamandan cewa ya zama Dan Gida,ya Kuma yi kira ga sauran ma’aikatan da suyi koyi da kyawawan hali irin na DD Auta kwamanda Mai tafiya,,yayi addu’ar Allah ya bamu lafiya da zama lafiya. Amen.

Allah ya taimaki sarki, ya karawa sarki lafiya. Amen.

Comr. Ubaliyo Falalu Gaya
Mashawarci ga Sarkin Gaya kan kafafen sada zumunta na zamani
18/12/2023.

Related Posts

Leave a Comment