361
Akalla ’yan kasuwa 11 da ke kai albasa da sauran amfanin gona daga karamar hukumar Goronyo ta Jihar Sakkwato zuwa Jihar Neja ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani hadari.
Lamarin wanda ya afku a ranar Litinin din da ta gabata a kan hanyar Maiyama/Koko a karamar hukumar Koko-Besse ta jihar Kebbi, hadarin ya raunata wasu fasinjoji kusan 50, wadanda a halin yanzu suke samun kulawa a asibiti.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubabar, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

