Wata daliba ‘yar Najeriya da ta kuduri aniyar kafa wani sabon tarihi a fannin wanki da hannu, an ga bidiyonta a lokacin da ta yi matukar canzawa.
Bidiyon Subair Enitan ya karade shafukan sada zumunta, inda aka gan ta kwance a gado tana hutawa bayan abin da ta ce ta kwashe sa’a 58 a ranar Litinin tana ta wanki, sannan ta rika nuna wa kawayenta hannuwanta da suka kode, suka yi fari fat, kuma duk sun yi tattara.
Zuwa yanzu masu kula da kundin bajinta na Guinness World, ba su ce uffan a kan yunkurin Subair Enitan ba, kamar yadda ta fada kafofin yada labarai a ranar Litinin:
Quote Message: Burina ya cika, na kammala wannan aiki a kan idon mahaifiyata da kawayena da kuma abokan aiki wadanda suka cika wurin nan, ba masaka tsinke don nuna kauna da goyon baya ga burina.”
Yunwar shiga kundin bajinta na duniya ta karade Najeriya a ‘yan watannin baya-bayan nan.
Shahararriyar mai girki Hilda Baci ce ta fara wannan salo, inda ta yi ta girki tsawon sa’a 93 babu kakkautawa, sai dai bayan wata biyar sai aka samu wani gwanin girki dan kasar Ireland, Alan Fisher da ya ture ta, daga kan matsayin, lokacin da ya yi girki tsawon sama da awa 119.
A baya-bayan nan ma, wata ‘yar Najeriya da ake kira Helen Williams ta kafa wani sabon tarihi wajen yin karin gashi da hannu mafi tsawo – da ya kai mita 351.28.

