Home Labarai Kotu ta sake tisa ƙeyar tsohon shugaban bankin Nigeria CBN Godwin Emefiele gidan kaso, bayan ya gaza cika ƙa’idojin Beli.

Kotu ta sake tisa ƙeyar tsohon shugaban bankin Nigeria CBN Godwin Emefiele gidan kaso, bayan ya gaza cika ƙa’idojin Beli.

by Muhsin Tasiu Yau

Go back

Your message has been sent

Warning
Warning
Warning
Warning

Warning.

 

Wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Abuja, ta ɗage shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan babban bankin ƙasar (CBN) zuwa watan Janairun shekara ta 2023, yayin da zai ci gaba da zama a gidan yari har sai ya cika ƙa’idar belinsa ta kuɗi naira miliyan 300.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ce ta gurfanar da Emefiele bisa zargin sa da laifuka shida, ciki har da zargin badaƙala da kuɗi naira biliyan 1.6.

Sai dai tsohon gwamnan babban bankin ya musanta zargin.

Yanzu kotun ta ayyana 18 ga watan Janairun 2024 domin sake zama kan shari’ar.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ne ya dakatar da Emefiele daga muƙaminsa a ranar 9 ga watan Yuli bayan “wani bincike da ake yi da kuma shirin sake fasalin ɓangaren kuɗi na ƙasar.

Related Posts

Leave a Comment