Home Labarai JAMI ‘AN “COMMUNITY WATCH” NA JAHAR KATSINA SUN FAFATA DA ƳAN BINDIGA

JAMI ‘AN “COMMUNITY WATCH” NA JAHAR KATSINA SUN FAFATA DA ƳAN BINDIGA

by Muhsin Tasiu Yau

…sun kashe wasu .wasu sun sha da kyar

Misbahu Ahmad Batsari

@ Katsina Times

Jami’an tsaron “community watch corps”sun fafata da ƴan bindiga a yankin Batsari ta jihar Katsina.

Da misalin ƙarfe 9:30pm na daren asabar 25/11/2023. ƴan bindiga masu tarin yawa suka kaima jami’an tsaron community watch corps dake aikin bada tsaro a ƙauyen Watangaɗiya hari.

Yan bindigar Sunyi ƙoƙarin yima jami’an tsaron ƙawanya amma jami an da hadin gwiwar mutane garin suka dake akayi ta ɗauki ba daɗi, inda ƴan bindigai suka dinga antaya masu harsasi da bindigar girke ,wasu kuma da AK-47,kamar yadda wani mutumin garin ya tabbatar da jaridun Katsina Times.

Related Posts

Leave a Comment