Home Labarai Kotun Ƙoli ta tsayar da ranar da za ta yanke hukunci kan shari’ar Farouk Lawan

Kotun Ƙoli ta tsayar da ranar da za ta yanke hukunci kan shari’ar Farouk Lawan

by Muhsin Tasiu Yau

Kotun Ƙoli ta tsayar da ranar 26 ga watan Janairu, 2024, a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan shari’ar tsohon ɗan Malajisar Wakilai, Farouk Lawan wanda yake tsare a gidan yari.

Kwamitin alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a John Okoro ya tsayar da wannan rana ne bayan da lauyoyin ɓangarorin da shari’ar ta shafa suka miƙa bayanansu ga kotun.

Lawan ya ɗaukaka ƙara ne inda yake neman Kotun ta shure hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta yanke a ranar 24 ga Fabrairun 2022 na wajabta masa zaman kurkuku na tsawon shekara biyar, kana ta wanke shi daga biyu cikin laifuka biyar da Gwamnatin Tarayya ke tuhumarsa masu nasaba da rashawa.

Duk da cewa buƙatar Lawan ta neman beli ce har zuwa lokacin da za a yanke hukuncin ɗaukaka ƙara, amma kotun ta zaɓi ta ɗauki babbar ƙarar maimakon sauraren ƙarar neman beli.

Yayin da yake roƙon kotun da ta fara gabatar da buƙatar belin, lauyan Lawan, Joseph Daudu, ya ce lafiyar wanda yake karewa na fuskantar barazana.

Daudu ya shaida wa kotun cewa Lawa na fama da cutar kansa wadda ta kai mataki na uku, ya ce idan aka bari cutar ta kai mataki na huɗu akwai yiwuwar a rasa Lawan.

Sai dai a nasa ɓangaren, lauyan Gwamnatin Tarayya, Bagudu Sanni, ya nemi Kotun Ƙolin da ta tabbatar da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke sannan ta yi watsi da ƙarar da Lawan ya shigar.

Babbar Kotun Tarayya a Abuja ce ta kama Lawan da laifuka uku a ranar 22 ga Yunin 2021, da suka haɗa da karɓar cin hanci na $500,000 daga hannun hamshaƙin ɗan kasuwar nan, Femi Otedola da sauransu.

Related Posts

Leave a Comment