Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Imo, Mista Hope Uzodimma, ya zargi shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC), Joe Ajaero, da yin katsalandan a harkokin siyasar jihar.
Idan dai za a iya tunawa, hukumar ’yan sandan jihar Imo ce ta kama Ajaero a ranar Laraba yayin da yake jagorantar wata zanga-zanga a babban birnin jihar, Owerri.
Duk da haka, ‘yan sanda sun ce “an kuɓutar da shi daga hannun gungun mutane kuma an keɓe shi a wani wuri mai tsaro.”
Daga baya NLC ta sha alwashin tattara mambobinta a jihar domin gudanar da yajin aikin gama-gadi domin nuna adawa da kamun da aka yi wa Ajaero.
Ƙungiyar ta kuma zargi Uzodimma da haɗa baki da kwamishinan ’yan sandan jihar, Muhammed Barde, don sace shugabansu.
Da yake mayar da martani, gwamnan ya zargi Ajaero da yin katsalandan a harkokin siyasar jihar.
Uzodimma ya yi wannan zargin ne a ranar Alhamis bayan karcar tutar jam’iyyar APC daga hannun shugaba Bola Tinubu a fadar Aso Rock Villa da ke Abuja.
Ajaero, yayin ganawa da manema labarai a farkon makon, ya zargi gwamnatin jihar Imo da tauye haƙƙin ma’aikatan Nijeriya a jihar, don haka ya sha alwashin haɗa kan ‘ya’yan ƙungiyar a jihar don gudanar da yajin aikin gama-gari.

