Home Labarai Za’a Samar Da Motoci Sama Da Milyan 11 Masu Amfani Da Gas

Za’a Samar Da Motoci Sama Da Milyan 11 Masu Amfani Da Gas

by Muhsin Tasiu Yau

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin samar da motoci miliyan daya masu amfani da Gas nan da shekarar 2027.

A cewar mashawarcin shugaban kasa na musamman kan harkokin samar da dabarun cigaban kasa, Toyin Subaru, ya ce motocin zasu temaka wajen saukaka yanayin zirga-zirga a kasar nan.

Ya kuma baiyana cewar ana saran samfurin motocin sama da guda dubu 11 zasu fara aiki a cikin wannan makon.

Subaru ya ba da tabbacin cewar fara sufurin motoci masu amfani da makamashin gas, zai temaka wajen karya farashin gas zuwa naira 230 akan kowanne kilogiram daya.

Related Posts

Leave a Comment