Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, ta fitar da sunayen ‘yan takarar gwamnan Bayelsa da Imo da aka yi wa gyaran fuska.
Bisa ga lissafin da aka yi wa gyaran fuska da hukumar ta wallafa a ranar Talata, ba a saka sunayen Timipre Sylva da abokin takararsa, Joshua Maciver na jam’iyyar All Progressives Congress ba a zɓen jihar Bayelsa.
Sakatariyar Hukumar, Rose Oriaran-Anthony ne ta sanya hannu a jerin sunayen.
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, an bar shafi na sunayen ɗan takarar Jam’iyyar APC da abokin takararsa tare da umarnin kotu a jiki.
Haka kuma a jihar Imo, hukumar ta haɗa da sunayen Uchechukwu Ishiodu a matsayin ɗan takarar gwamna da Ahumbe Chiazor a matsayin abokin takarar jam’iyyar Peoples Redemption Party a zaɓen jihar.
Ta ce bayan wallafar, an ba wa hukumar umarnin kotu game da tsayar da ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa.
An sabunta jerin sunayen ‘yan takara dangane da zaɓen gwamnan jihar Bayelsa na 2023 bisa ga umarnin kotu da hukumar ta bayar,” in ji Oriaran-Anthony.
A ranar 10 ga watan Oktoba ne babbar kotun tarayya da ke Abuja ta haramta wa Sylva shiga zaɓen gwamnan jihar.
- Mai shari’a Donatus Okorowo, a hukuncin da ya yanke, ya ce Sylva da aka rantsar da shi sau biyu kuma ya yi mulki na tsawon shekaru biyar a matsayin gwamnan jihar Bayelsa, zai saɓa wa kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima idan ya sake tsayawa takara.


