Home Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Sarkin Ƙasar Ebira, Ado Ibrahim ya kwanta dama yana da shekara 94.

Da Ɗumi-ɗumi: Sarkin Ƙasar Ebira, Ado Ibrahim ya kwanta dama yana da shekara 94.

by Muhsin Tasiu Yau

Allah Ya yi wa Sarkin Ƙasar Ebira (Ohinoyi of Ebiraland), Dokta Ado Ibrahim, rasuwa.

MANHAJA ta tattaro cewar Basaraken ya rasu ne da safiyar Lahadi, inda ya bar duniya yana da shekara 94.

Majiyarmu ta ce marigayin ya rasu ne a wani asibitin Abuja inda yake jinya.

Majiyar ta ce za a yi jana’izar marigayin a wannan Lahadin a Okene babbar cibiyar Masrautar Ebira a Jihar Kogi.

An haifi marigayin ne a ranar 7 ga Fabrairun 1929, kuma ya zama sarki ne a ranar 2 ga Yunin 1997.

Related Posts

Leave a Comment