Hajiya Farida Musa Kallah, mace ‘yar kasuwa mai burin ta zama Ɗangote a mata ta ce babban burinta shi ne a ce ita ce ta ɗaya a manyan ‘yan kasuwa mata a tsakanin baƙaƙen fata na duniya, kamar yadda Alhaji Aliko Ɗangote ya ke matsayin ɗan Afrika baƙar fata mafi kuɗi a duniya.
Hajiya Farida wadda ita ce shugabar kamfanin saye da sayarwa na kayyakin buƙatun yau da kullum na al’umma, ta bayyana haka ne a lokacin taron qungiyar ‘yan kasuwa mata ta mu inganta sana’armu wanda aka gabatar a Unguwar GRA dake Kano a tsakiyar makon nan.
Haka kuma ta ƙara da cewa wannan kasuwanci nata ta fara tun daga cikin gida ne har Allah ya albarkaci wannan kasuwanci ta fito waje, inda yanzu haka ta zama ɗaya daga cikin ‘yan kasuwa masu ɗaukar matasa maza da mata domin ba su aiki a kamfanin ta na FMK da ke birnin Kano.
Haka kuma ta ƙara da cewa akwai buƙatar mata su fito domin yin kasuwanci daidai da yadda shari’a da al’adarmu ta shimfiɗa domin hakan zai kawo ragowar matsalolin aure da zamantakewa a tsakanin iyali kuma mace idan tana kasuwanci wani abu ne da zai sa ‘ya’yanta su zama a wuri ɗaya ta yadda za a samu kyakkyawar tarbiyya a tsakanin iyalai.
Haka kuma ta ce akwai buƙatar neman ilimin addini da na zamani domin bunƙasa tarbiyya da kuma kyautata rayuwa ta kasuwanci da sauran mu’amala.
A ƙarshe ta yaba wa shugabar ƙungiyar Hajiya Maryam Abbas Abdulkadir Bichi, kan jagorantar shirya wannan taro na haɗa kan mata da suka fito domin taka muhimiyar rawa wajen cigaban kasuwancinsu.
FMK ta ce akwai kuma buƙatar gwamnatoci na Arewa su tallafa wa mata domin cigaban kasuwancinsu, domin a cewarta matan Arewa suna da ƙoƙari wajen neman halalinsu da kuma jajircewa a kasuwanci kuma matan Arewa ne ɗaukaka da kuɗi baya hanasu biyayya ga mazajensu domin kyakkyawan tsarinmu na addini da al’adunmu na Arewa.

