A wasan da Ferran Torres ya zura ƙwallo ya bayar da ɗaya aka zura a raga a bai wa Barcelona damar doke Shakhtar Donetsk da ci 2-1.
Ƙungiyoyin sun buga wasa na uku-uku a cikin rukuni na takwas a Champions League.
Torres ne ya fara cin ƙwallo a minti na 28 da take leda, bayan da ya Fermin Lopez ya buga ƙwallo ta gefen raga sai ta koma ta wajensa shi kuma ya zura a raga.
Daga baya tsohon ɗan wasan Manchester City, ya bai wa Lopez ƙwallon da ya zura a raga a minti takwas tsakani.
Shakhtar ta zare ɗaya ta hannun Heorhii Sudakov, bayan da suka sha ruwa suka koma zagaye na biyu a fafatawar.
Barcelona, wadda rabonta da ɗaukar Champions League tun 2015 tana ta daya a kan teburin rukuni na uku da maki tara.
Ita kuwa Shakhtar tana ta uku da tazarar maki shida tsakaninta da ƙungiyar Sifaniya mai riƙe da kofin La Liga na bara.

