Daga BASHIR ISAH
Masarautar Zazzau ta naɗa Alhaji Mu’azu Nuhu Bamalli a matsayin sabon Magajin Garin Zazzau.
Bayanin naɗin na ƙunshe ne cikin sanarwar da masarautar ta fitar a ranar Juma’a mai ɗauke da sa hannun Jami’in Yaɗa Labarai, Abdullahi Aliyu Kwarbai. Ubangiji
Alhaji Mu’azu yayan tsohon Magajin Garin Zazzau, Ambasada Mansur Nuhu Bamalli ne wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Juma’a ta makon jiya.
Kafin sabon naɗin nasa, Alhaji Mu’azu Nuhu Bamalli shi ne Baraden Zazzau.
Sabon Magajin Garin na Zazzau Darakta ne a Babban Bankin Nijeriya kuma ƙani ga Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR
A hannu guda, Sarkin Zazzau ya naɗa Alhaji Aliyu Nuhu Bamalli (SAMBO) a matsayin sabon Baraden Zazzau.
Duka naɗe-naɗen sun fara aiki ne nan take, in ji sanarwar.

