Home Labarai Emefiele ya faɗa komar EFCC jim kaɗan bayan kuɓuta daga hannun DSS

Emefiele ya faɗa komar EFCC jim kaɗan bayan kuɓuta daga hannun DSS

by Muhsin Tasiu Yau

Daga BASHIR ISAH

A halin da ake ciki, tsohon Shugaban Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, na tsare a hannun Hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC don amsa tabayoyi da fuskantar bincike.

Majiyarmu ta ce ta samu tabbacin Emefiele na can babban ofishin EFCC da ke Jabi, Abuja, bayan da jami’anta suka ɗauke shi cikin dare a ranar Alhamis jim kaɗan bayan da hukumar DSS ta sako shi.

Majiya mai tushe ta ce EFCC ta damƙe Emefiele ne bisa zargin aikata ba daidai ba a lokacin da yake shugabancin CBN.

“Tabbas, yanzu haka Emefiele na tsare a hannunmu (EFCC), a daren da ya gabata aka tsare shi jim kaɗan bayan da DSS ta sako shi.

“Yana kan amsa tambayoyi a yanzu haka a babban ofishin hukumar (EFCC), inda ake bincikarsa kan zargin karkatar da kuɗaɗe da sauransu a lokacin da yake shugabancin CBN,” in ji majiyar.

Sai dai duk ƙoƙarin da aka yi don jin ta bakin mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale a hukumance hakan ya ci tura.

Idan za s iya tunawa tun a watan Yunin da ya gabata DSS ke tsare da Emefiele bayan da Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi.

Related Posts

Leave a Comment