399
Wata Mata Ta Siyar da Jikanta Kan Kudi N50,000 a Anambra
Wata mata ta siyar da jikanta mai watanni uku a duniya a kan kuɗi N50,000 a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa wacce ake zargin Oluchukwu Nwosu ta siyar da jaririn ne ba tare da sanar da ɗiyarta Ijeoma ba, wacce ta haifi yaron ba tare da aure ba.
Chidinma Ikeanyionwu, hadimar kwamishiniyar mata da walwalar jama’a a jihar, Ify Obinabo, ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, 22 ga watan Oktoba.
Ikeanyionwu ta ce a yanzu kwamishinan ta ceto yaron, sannan ta kuma taimaka wajen sanya ƴan sanda cafke wacce ake zargin.

