Home Labarai An buɗe mashigin Rafah don kai agaji ga fararen hula a Gaza.

An buɗe mashigin Rafah don kai agaji ga fararen hula a Gaza.

by Muhsin Tasiu Yau

An buɗe mashigin kan iyakar Rafah da ke tsakanin Gaza da Masar domin kai kayan agaji ga dubban fararen hula.

An ga manyan motoci ɗauke da kayan agaji na shiga ta kan iyakar daga Masar zuwa Gaza.

Kawo yanzu ba a san tsawon wane lokaci mashigin zai ɗauka a buɗe ba.

Isra’ila ta amince da barin manyan motocin 20 shiga zuwa Gaza.

Majalisar Dinkin Duniya ce ta yi kiran buɗe kan iyakar domin isar da kayan agaji ga fararen hular da ke cikin tsananin buƙatar tallafin.

Related Posts

Leave a Comment