Home Labarai Tinubu ya naɗa Adewale Adeniyi shugabancin Hukumar Kwastam.

Tinubu ya naɗa Adewale Adeniyi shugabancin Hukumar Kwastam.

by Muhsin Tasiu Yau

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Adewale Adeniyi a matsayin sabon shugaban Hukumar Yaƙi da Fasaƙwauri ta Nijeriya (NCS).

Sanarwar da ta fito ta bakin Daraktantan yaɗa labarai na ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey, ta ce naɗin ya soma aiki ne daga ranar 19 ga Otoban 2023.

Idan za a iya tunawa, a watan Yulin da ya shige Shugaba Tinubu ya naɗa Adeniyi riƙon ƙwaryar shugabancin hukumar ta Kwastam kana ya yi wa wasu jiga-jigan hukumar ritaya.

Kazalika, naɗin ya shafi wasu jami’an hukumar da aka ɗaga matsayinsu zuwa mataimakan Kwantrola Janar.

Jami’an da naɗin ya shafa sun haɗa da: DCG FO Okun, DCG MBA Musa da DCG A Hamisu, ACG K Olumoh da ACG AB Mohammed da ACG A Alajogun.

 

Related Posts

Leave a Comment