Home Labarai LABARI‘Rage Dogaro da Man Fetur Ne Kadai Hanyar Shawo Kan Matsalar Cire Tallafi’, Sunusi Lamido.

LABARI‘Rage Dogaro da Man Fetur Ne Kadai Hanyar Shawo Kan Matsalar Cire Tallafi’, Sunusi Lamido.

by Muhsin Tasiu Yau

Tsohon Sarkin Kano, Sunusi Lamido Sunusi ya ce rage dogaro da man fetur ita ce kadai hanyar magance matsalar cire tallafin mai.

Sunusi ya bayyana haka ne a jiya Alhamis 19 a watan Oktoba yayin gabatar da lakca a jihar Legas,cewar TheCable.

Meye Sunusi ya ce kan cire tallafin mai?

Tsohon Sarkin ya ce ‘yan Najeriya sun dade su na maganan cire tallafi tun shekakar 2011 lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan.

Ya ce arzikin mai kadai bai isa ya mayar da kasar mai arziki ba amma kuma ya kai ya shigar da mu cikin matsaloli a Najeriya.

Ya ce:

“Mun fada idan ba mu yi wani abu ba kan wannan cire tallafin, za mu kara dawo wa inda mu ke ne a yanzu.

“Babban abin da zai shawo kan wannan matsalar ta cire tallafi shi ne rage dogaro da man fetur a kasar.

“Masana tattalin arziki sun ce Najeriya ba za ta taba zama mai arziki ba kawai don samar da mai da ta ke musamman idan aka kwatanta da Saudiyya.”

Wane gargadi Sunusi ya bayar kan sauraran masana?

Tsohon gwamnan CBN ya ce Saudiyya na fitar da gangan mai 91 ga kowa ne mutum daya a shekara yayin da Najeriya ke fitar da ganga 2.3.

Ya kara da cewa kasar Kuwait na cire ganga 221 yayin da kasar Gabon da ke Nahiyar Afirka ke cire ganga 31.7.

Sunusi ya ce gwamnatin ba ta shirya kawo gyara ba tun da ba ta sauraran masana tattalin arziki inda ya ce babu yadda za a yi kullum ana abu daya a yi tsammanin sakamako daban, cewar Premium Times.

Related Posts

Leave a Comment