Home Labarai Dalilin Sanata Ndume na ficewa daga zauren Majalisa a fusace.

Dalilin Sanata Ndume na ficewa daga zauren Majalisa a fusace.

by Muhsin Tasiu Yau

Da alama dai abubuwa ba su tafiya yadda ya kamata wa Majalisar Dattawan Nijeriya musamman ganin yadda shugabanin majalisar suka shiga ganawar sirri mintoci ƙalilan da fara zaman majalisar a ranar Talata.

Yayin zaman Majalisar a ranar Talata an ga Mai Tsawatarwa na Majalisar, Sanata Ali Ndume (APC Borno ta Kudu), ya yi ƙoƙarin nusar da Majalisar dangane da kurakuran da ake zargi Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ya tafka ba tare da an yi gyara ba.

Kuskuren da Ndume ke nufi shi ne kan batun ƙudirin da Sanata Summaila Kawu (NNPP Kano ta Kudu) ya gabatar a majalisa kan buƙatar da ke akwai na tafka muhawara a kan batun sake buɗe iyakar Nijeriya da Nijar, ba tare da soma karanto taken ƙudirin ba.

Related Posts

Leave a Comment