Home Labarai Wani ɗan Nijeriya mai shekaru 70 da haihuwa, Injiniya Hadi Usman, ya samu lambar yabo ta digirin digirgir a fannin kimiyya daga jami’ar jihar Gombe bayan ya ƙirqƙiro injin janareta maras amfani da fetur. A cewar babban mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga gwamnan jihar Gombe, Safianu Danladi Mairiga akan manhajar X, an bai wa Usman wannan digiri ne a taron da aka kammala na 10, 11, 12, da 13 na jami’ar jihar Gombe.

Wani ɗan Nijeriya mai shekaru 70 da haihuwa, Injiniya Hadi Usman, ya samu lambar yabo ta digirin digirgir a fannin kimiyya daga jami’ar jihar Gombe bayan ya ƙirqƙiro injin janareta maras amfani da fetur. A cewar babban mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga gwamnan jihar Gombe, Safianu Danladi Mairiga akan manhajar X, an bai wa Usman wannan digiri ne a taron da aka kammala na 10, 11, 12, da 13 na jami’ar jihar Gombe.

by Muhsin Tasiu Yau

Wani ɗan Nijeriya mai shekaru 70 da haihuwa, Injiniya Hadi Usman, ya samu lambar yabo ta digirin digirgir a fannin kimiyya daga jami’ar jihar Gombe bayan ya ƙirqƙiro injin janareta maras amfani da fetur.

A cewar babban mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga gwamnan jihar Gombe, Safianu Danladi Mairiga akan manhajar X, an bai wa Usman wannan digiri ne a taron da aka kammala na 10, 11, 12, da 13 na jami’ar jihar Gombe.

Hadi wanda aka ce bai taɓa zuwa makarantar boko ba, ya kafa gidan rediyo, da na’urar watsa labarai ta rediyo. Sannan ya zama gidan rediyon al’umma a watan Janairun 1980.

Danladi ya bayyana cewa, Hadi ya kuma gina janareta wanda ba ya aiki da man fetur.

Ya ƙara da cewa, ɗan asalin unguwar Jekadafari da ke ƙaramar hukumar Gombe, jihar Gombe ya haddace Alƙur’ani mai girma yana ɗan shekara 12.

A halin da ake ciki dai, ‘yan Nijeriya da dama sun yaba wa hazaƙar mutumin tare da yin kira ga gwamnati da ta amince da fasaharsa.

Related Posts

Leave a Comment