Home Labarai Tinubu ya rantsar da ƙarin ministoci uku.

Tinubu ya rantsar da ƙarin ministoci uku.

by Muhsin Tasiu Yau

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya rantsar da ƙarin ministoci guda uku a cikin majalisarsa.

Minitocin da rantsawar ta shafa sun haɗa da Jamila Bio Ibrahim da Ayodele Olawande da kuma Balarabe Lawal.

An rantsar da su ne a zauren Majalisar Zartarwa gabanin zaman majalisar wanda Shugaba Tinubu ya jagoranta a ranar Litinin.

Sabbin ministocin sun sha rantsuwar kama aiki ne makonni biyu bayan da Majalisar Dattawa ta tantance su.

Tuni dai Shugaban Ƙasa ya miƙa wa kowannensu ma’aikatar da zai riƙe: Jamila Bio-Ibrahim – Babbar Minista Matasa, Ayodele Olawande – Ƙaramin Ministan Matasa, sannan Balarabe Lawal – Ministan Muhalli.

Related Posts

Leave a Comment