Home Labarai Ma’aikatan NIPOST sun hana sabon shugaban da Tinubu ya naɗa musu shiga ofis.

Ma’aikatan NIPOST sun hana sabon shugaban da Tinubu ya naɗa musu shiga ofis.

by Muhsin Tasiu Yau

Ma’aikatan Hukumar Tura Saƙonni (NIPOST) a babban ofishin hukumar da ke Abuja, sun yi zanga-zanga tare da rufe ma’aikatar saboda rashin amincewa da naɗa Tola Odeyemi a matsayin sabon shugaban hukumar da Shugaba Bola Tinubu ya yi.

A makon da ya gabata Kakakin Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, ya bada sanarwar cewa Shugaba Tinubu ya yi sabbin naɗe-naɗe a hukumomin sadarwa ciki har da hukumar NIPOST.

Sai dai jim kaɗan bayan sanar da naɗin Odeyemi, rahotanni suka nuna an sake maida babban jami’in hukumar da aka tsige da fari.

An ga Adepoju a cikin wani faifan bidiyo da aka yaɗa yana yi wa ma’aikata jawabi inda ya yi iƙirarin Tinubu ya maida masa kujerarsa.

Ana haka ne a ranar Litinin, sai aka ga ma’aikatan hukumar sun hana sabon shugaban hukumar shiga ma’aikatar suna masu cewa naɗin nasa ya saɓa wa muradinsu.

Majiyarmu ta ce yayin zanga-zangar tasu, an jiyo ma’aikatan na cewa Adepoju shi ne zaɓinsu.

Related Posts

Leave a Comment