Home Labarai Ba da jimawa ba za a fara shiga daji da ni – Gwamna Raɗɗa.

Ba da jimawa ba za a fara shiga daji da ni – Gwamna Raɗɗa.

by Muhsin Tasiu Yau

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewar, da zarar an kammala duk shirye-shiryen da suka dace za a fara shiga daji da shi don farautar ‘yan fashin daji.

Gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata hira da ya yi da BBC.

“Nan ba da jimawa ba idan an kammala duk shirye-shiryen da suka dace za’a fara shiga daji da ni,” inji Shi.

Gwamnan ya ci gaba da cewa, zai iya sadaukar da rayuwarsa domin kawo ƙarshen matsalar ‘yan bindigar da suka addabi jihar.

Don haka ne ya ƙuduri aniyar ganin bayan ‘yan bindigar da suka addabi jihar cikin amincewar Allah.

Raɗɗa ya kuma ce, ɓangaren tsaro shi ne ya fi kowanne muhimmanci kuma tuni suka fahimci hakan shi ya sa ma aka yi doka don a kafa rundunar ‘yan sa-kai tare da ba su makamai da nufin taimaka wa jami’an tsaro a jihar.

Ya ce, ”To yanzu mun ƙaddamar da su, mun horar da su, mun ba su kayan aiki mun ba su motoci da babura da ma motoci masu sulke.”

Dangane da biyan su albashi kuwa Gwamnan ya ce, biyansu kuɗaɗen alawus, gwamnatinsa ta ɗauki tsarin mafi ƙarancin albashi wanda da shi ne za a rinƙa biyan ‘yan sa kan alawus.

Kazalika, Raɗɗa ya bayyana cewar wani abu da ya kamata mutane su sani shi ne, su waɗannan ‘yan sa kan su ne waɗanda a garuruwansu suke irin wannan aiki ba tare da an biya su ko sisi ba, kuma suna waɗannan ayyuka ne saboda su kare mutuncin iyayensu da ‘yan uwansu da kuma danginsu.

“Batun da wasu ke yi cewa irin waɗannan ‘yan sintiri su ke ƙara dagula al’amura a harkar tsaro, zance ne na banza domin duk wanda ke zaune a wuraren da ke fama da matsalar tsaro ya san abin da ke faruwa, ta yaya za a kare mutanen da ke sace mutane su ci mutuncinsu da kashesu, ai ba abu ne mai wuya ba.” Inji Gwamnan.

Ya ƙara da cewa, sai dai ran shi ya fita a kan ya yarda wani ya zo ya ci mutuncin al’umar jihar.

“Wallahi tallahi a matsayina na gwamna sai dai raina ya fita ba zan yarda wani ya zo ya ci mutane ba bayan ina da yadda zan yi, don wannan matsala ta kai halin da dole a haɗa kai domin ganin cewa an kawo ƙarshen wannan matsalar don matsala ce da ta dame mu.” Inji shi.

Gwamnan jihar ta Katsina ya kuma ce duk wanda ke wani surutu akasin hakan, yana yi ne saboda ba ‘yan uwansa ake kashewa ba.

← Back

Thank you for your response. ✨

Related Posts

Leave a Comment