Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya a Jihar Benuwai ta sallami wani ɗan sanda mai suna Belasa Iyangedue bisa zargin sa da yi wa wata yarinya ’yar shekara 16 fyaɗe a lokacin da ta ke tsare a ofishin ‘yan sanda.
An rawaito cewa kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Batholomew Onyeka ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke Makurdi.
Onyeka ya ce rundunar ’yan sandan Nijeriya a matsayinta ta hukuma mai ƙoƙarin tabbatar da ɗa’a ba za ta amince da irin wannan laifin da ya saba wa ƙa’idojin aikin ba.
Ya bayyana cewa ɗan sandan da aka kora ya aikata laifin a ofishin ’yan sanda na Tse Agbaragba da ke ƙaramar hukumar Konshisha a jihar kuma tuni ya fuskanci hukunci.
Rahoton da aka samu daga kotun Majistare Makurdi ya bayyana cewa ɗan sandan ya aikata laifin ne a ranar 16 ga watan Agustan 2023 da misalin ƙarfe 2 na rana.
A yayin da ake gudanar da bincike bayan an kama Iyangedue, ya amsa laifin da ya aikata wanda ya saɓa wa sashe na 284 na dokokin jihar Binuwai na shekarar 2004.

