Jaridar daily post ta rahoto cewa an yi garkuwa da daliban ne a gidansu da ke unguwar Sabon Gida Damba a karamar hukumar Gusau.

Jami’in yada labarai na rundunar ‘Operation Hadarin Daji, Captain Yahaya Ibrahim, ya shaidawa manema labarai a Gusau cewa, sojojin sun amsa kiran gaggawa inda suka tare duk wasu manyan hanyoyin fita na ‘yan ta’addan tare da yin artabu da ‘yan ta’addan, lamarin da ya yi sanadiyar ceto daliban makarantar hudu.