580
Kotun soja ta ɗaure Daraktan kamfanin kula da kadarorin Sojojin Nijeriya, Manjo Janar Umaru Mohammed, shekar bakwai a gidan yari bayan da ta kama shi da laifin sace kuɗaɗen gwamnati.
Kazalika, kotun ta kuma umarci mai laifin da ya maido da kuɗaɗe Dalar Amurka 2,178,900 da Naira biliyan 1.65 da ya sata.
Kotun wadda ke zamanta a Abuja, ta yanke hukuncin ne a ranar Talatar da ta gabata.
An kama Mohammed da laifuka 14 daga cikin laifuka 18 da ake zarginsa da aikatawa, da suka haɗa da karkatar da kuɗaɗen gwamnati, amfani da bayanan ƙarya, haɗin baki da dai sauransu.
Alƙalan kotun ƙarƙashin jagorancin Manjo Janar James Myam, sun bayyana cewa lauyan mai gabatar da ƙara ya gabatar da shaidu 24 yayin mai kare kansa ya gabatar da shaidu biyu kacal.


