Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa, halin da duniya ke ciki a yau a cikin kowane mutum takwas za a tarar da guda na fama da taɓin hankali.
Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres ne ya nayyana haka cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata albarkacin Ranar Lafiyar Ƙwaƙwalwa ta Duniya ta bana.
Sakataren ya bayyana lafiyar ƙwaƙwalwa a matsayin mai muhimmanci wanda da ita rayuwa kan inganta, haka ma da ita al’umma take bunƙasa.
Ya ƙara da cewa, mata da matsa na daga cikin waɗanda ake samu suna fama da matsalar taɓin hankali. Ya ce, masu fama da wannan matsalar kan fuskanci tsangwama a cikin al’umma.
A cewarsa, “Lafiyar ƙwaƙwalwa ba samun dama ba ne, ‘yanci ne na ɗan Adam. Kuma dole hakan ya zama ɓangare na kiwon lafiya a faɗin duniya.”
Ya ce wajibi ne gwamnatoci su riƙa bai wa al’umma kulawar da za ta maido musu sa lafiyarsu da kuma kare musu ‘yancinsu.
Kazalika, ya ce ya zama dole a daƙile dalilan da ke sabauto wa al’umma talauci, tada ƙayar baya, nuna wariya da sauransu, sannan a bada himma wajen ƙirƙiro abubuwan da za su yauƙaƙa al’umma.

