Daga MUHSIN TASI’U YAU
An sace ‘Dalibai Hudu (4) ‘yan jami’ar Nasarawa State University, Keffi (NSUK) Wanda wasu mutane da ba’a San ko su Wane ba ‘dauke da muggan makamai suka sace su.
Al’amarimln ya faru ne a kusa da unguwar Angwan Kare Bayan BCG
‘Daya Daga cikin wanda suka ga faruwar wannan al’amari a Idon sa yace abun ya faru da misalin 10:30pm
Daga cikin ‘daliban da aka dauka akwai Mai suna Rahila Hanya -SLT100 Level, Josphine Gershon ‘Dalibin Computer Science 100 Level Rosemary Samuel- Business Administration 100 Level Da kuma Goodness Samuel -Geography 100 Level.
Da faruwar wannan al’amarin ne cikin rubatacen jawabi Daga Daily Post, Wanda Shugaban ‘Kungiyar ‘daliban Comrade
Oshafu Nuhu Abdurrahman yai Kira ga ‘dalibai da su kwantar da hankalin su su raja’a cikin Addu’a da rokon Allah ya dawo dasu cikin Lafiya da kwanciyar hankali.
Sannan ya ‘kara da sanarwar duk wani ‘dalibi da ya zauna cikin shiri duk sanda yaji wani abun a makaranta wanda bai gamsu da shi ba ya gaggauta sanar da hukuma sannan kuma abar hukumar tai aikin ta.

