Daga AMINA YUSUF ALI
Rukunin kamfanoni na BUA ya ba da sanarwar rage farashin kamfani na sumunti i zuwa Naira 3,500 kowacce jaka.
A halin yanzu dai ana sayar da shi a kan farashin kamfani na Naira 4,650, a kasuwa kuma ana sayar da shi Naira 5,000.
A wani jawabi da kamfanin ya gudanar a ranar Lahadi, kamfanin ya sanar da cewa, sabon farashin zai fara aiki a ranar Litinin ɗin da ta gabata kamar yadda muka gani.
Wani ɓangare na jawabin kamfanin mai taken, ‘Ragi a farashin sumuntin BUA’ ya bayyana cewa:
“Kamar yadda muka faɗa a sanarwarmu ta baya, game da manufarmu ta rage farashin sumunti bayan kamamla sababbbin layukanmu a ƙarshen shekarar nan, domin sauƙaƙa kayan aikin gine-gine.
Jawabin ya cigaba da cewa, wannan hukunci na rage farashin sumuntin ya biyo bayan cigaba da bunƙasa rassansa da kamfanin BUA ɗin ya yi.
Kuma a cewar jawabin ma, bayan kammala wasu rassansa da yake yi a halin yanzu, waɗanda za su dinga samar da Tan ɗin suminti miliyan 17 a kowacce shekara, kamfanin na BUA zai sake duba yiwuwar zaftare farashin sumuntin nan da watannin farko na shekarar 2024.
Amma a kula, duk wata tsohuwar oda wacce aka biya, amma ba a amshi kaya ba ita ma tana matsayin sabon farashin Naira 3500.
“Muna so dilolinmu masu lasisi kuma su tabbatar da masu saya sun amfana da farashin kamfani domin za mu sa ido a inda ake cinikin ɗai-ɗai domin tabbatar da biyayya ga sabon farashin”. A cewar sanarwar.
“A taƙaice dai, ana sa ran yanzu tunda farashin sarin kamfani ya kama Naira 3,500, ana ganin za a iya sayar da ɗai-ɗai a kan Naira 3,850 da N4,000”, a cewar wani dilan sumunti mazaunin Abuja.
Amma fa a cewar dilan, hakan kaɗai na iya faruwa ne idan kamfanin ya cika alƙawarinsa, su kuma diloli suka girmama wannan sabon farashin.
Da ma dai tun a watan da ya gabata ne a wata ziyara da ya kai wa shugaba Bola Ahmad Tinubu a fadarsa ta Aso Rock, shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul-Samad Rabiu, ya sanar da manema labarai na fadar cewa, zai rage farashin sumuntin kuma son taimaka wa ƙoƙarin gwamnatin, kamfanin zai sake buɗe manyan sassa guda biyu a ƙarshen shekarar nan ko a farkon shekarar baɗi.
Sai dai kuma duk da wannan gata da wannan attajiri ya yi wa ‘yan Nijeriya, har yanzu wasu suna sayar da shi a tsohon farashi. Idan an yi magana sai ka ji sun ce ai tsohon kaya ne.
Duk kuwa da kamfanin ya ba da sanarwar duk wani tsohon kaya da aka yi oda in dai ba a amsa ba, shi ma ya shiga layin sabon farashin

