DA YAWAN MATASAN MU NA FAMA DA DEPRESSION.
Aliyu Samba
A kullum idan na farka da safe na leƙo wannan sahar ta facebook, ina cin karo da rubuce rubucen da suke bayyana damuwa mai tsanani daga wanda suka yi su, gundarin sakon da ke cikin maganar su zai nuna maka ko dai tsananin damuwa (Depression) ko kuma abinda ake cewa (Frustration). Sai ka keɓe tsakanin ka da mutum da sunan tattaunawa musamman akan rayuwar sa, zaka gane Lallai abinda na faɗa ɗin nan gaskiya ne.
Me ya ke jawowa matasa depression ɗin nan?
Wasu daga ciki yanayin rayuwa ne ya jawo musu, wasu family issues (Matsalar dangi, iyali, iyaye, ko kuma ƴan uwa), wasu kuma kawai rashin godiyar Allah ne bisa ni’imomin da ya musu, wasu kuwa rashin haƙuri da kai zuciya nesa, wasu ƙiyayya ce da hassada take jefa su musamman idan suka ga wanda basa so cikin ni’ima da kwanciyar hankali, wasu kuma kawai rashin sanin kai ne, wasu matsala ce ko daga wajen aiki ko abokan mu’amala ko wadanda suke so (Saurayi/Budurwa), wasu kuma rashin kuɗi, wasu kuma rashin aiki, haka dai da sauransu.
Irin wannan yanayi shine ya sanya zaman lafiya ƙaranci, babu kyakkyawar fahimta tsakanin mutane, babu uzuri, babu ƙauna da soyayya don Allah, babu kyautatawa juna zato, babu kawaici da yakana, ayyukan ma da mutum yake yi kwata kwata basa tafiya yadda ya kamata, da sauran matsalolin da muke gani a kewaye da tsarin zamantakewar mu a yau. Da yawan matasa maza da mata suna fama da ɗayan waɗannan matsalolin, kuma cikin su suke wuni, su kwana su tashi babu wata mafita garesu.
A duk sanda ka zama mai hangen na gaba da kai kawai, baka taɓa kallon wanda ke ƙasa da kai, ba shakka ka ɗaura alaƙa mai ƙarfi da damuwa. Sai mun koyawa kan mu ƙana’a da kuma kallon waɗanda muka fi tare da nuna godiyar Allah bisa ni’imar sa garemu, sai mun yi haƙuri mun fahimci cewa rayuwar nan kowa da yadda yake fafutukar ganin ta inganta, sai mun yarda da cewa mu duka mutane ne, yan uwa ne koda kuwa mun saɓa a wasu ra’ayoyi da akidu, sai mun cire wa kan mu ƙiyayya, ƙyashi, hassada da mugun nufi akan mutane, sai mun yarda kowa rabon sa yake ci a wannan duniyar, in ba haka ba kuwa zamu ƙare cikin yanayi irin wannan mu rasa samun mafita a rayuwar mu.
Muyi hakuri da rayuwa, mu sani cewa rabon mu bazai taba wuce mu ba, da wannan zamu samu waraka daga tsananin damuwar da ta addabe mu, amma idan muka tafi a akasin haka, zamu wayi gari damuwar ta juye zuwa hawan jini ko bugun jini/zuciya, Allah ya kiyaye. A kuma dinga ziyartar likitan ƙwaƙwalwa lokaci bayan lokaci
#WorldMentalHealthDay2023
372


