Home Labarai Tawagar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ta isa Abuja domin kammala tattaunawa kan yiwuwar ɗage takunkumin hana bai wa ‘yan Nijeriya bizar shiga ƙasar. Tawagar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa wacce ta ƙunshi jami’an jihohi irinsu Alshehhu Rasheed, Teo Teck San, Almannaei Khalid, Alhosani Talal, da Janahi Asma sun isa Nijeriya a ranar Lahadi.

Tawagar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ta isa Abuja domin kammala tattaunawa kan yiwuwar ɗage takunkumin hana bai wa ‘yan Nijeriya bizar shiga ƙasar. Tawagar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa wacce ta ƙunshi jami’an jihohi irinsu Alshehhu Rasheed, Teo Teck San, Almannaei Khalid, Alhosani Talal, da Janahi Asma sun isa Nijeriya a ranar Lahadi.

by Muhsin Tasiu Yau

Tawagar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ta isa Abuja domin kammala tattaunawa kan yiwuwar ɗage takunkumin hana bai wa ‘yan Nijeriya bizar shiga ƙasar.

Tawagar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa wacce ta ƙunshi jami’an jihohi irinsu Alshehhu Rasheed, Teo Teck San, Almannaei Khalid, Alhosani Talal, da Janahi Asma sun isa Nijeriya a ranar Lahadi.

Tawagar da ake sa ran za ta gana da shugaba Bola Ahmed za ta kuma tattauna batun fara zirga-zirgar jiragen sama tsakanin ƙasashen biyu.

Tattaunawar ta Shugaba Tinubu a lokacin da ya kai ziyara a Abu Dhabi, babban birnin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, tare da Shugaba Mohamed bin Zayad al Nahyan, ya mayar da hankali ne kan maido da hulɗar diflomasiyya ƙasashen biyu.

Ana sa ran wannan tattaunawar za ta buɗe aofa ga zirga-zirgar jiragen sama na Emirates, ciki har da jirage 21 na mako-mako tare da jirage biyu na yau da kullum daga Dubai zuwa Legas da kuma jirgi ɗaya daga Dubai zuwa Abuja. Jiragen saman Air Peace zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa ma za su cigaba da zirga-zarga.

Idan za a iya tunawa, UAE a shekarar 2022, ta janye kamfanoninta na jiragen sama, Emirates da Etihad Airways, daga aiki a Nijeriya tare da dakatar da bayar da biza ga ‘yan Nijeriya sakamakon kuɗaɗen shigar da Emirates ke samu a Nijeriya ba tare da turawa kamfanin jirgin ba.

Related Posts

Leave a Comment