Ƙungiyar SERAP ta maka shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da wasu tsofaffin gwamnoni tara da ke a majalisar dattawa ta 10 bisa zargin karɓar kuɗaɗen fansho, yayin da suke karɓar albashi a matsayin sanatoci.
A cikin ƙarar wacce lauyoyin ƙungiyar, Kolawole Oluwadare da Ms Valentina Adegoke, suka shigar, akwai tsohon gwamna Dave Umahi, wanda tsohon Sanata ne, wanda yanzu ya zama ministan ayyuka.
Sauran sanatocin da aka sanya a ƙarar su ne, Abdulaziz Yari, Aminu Tambuwal, Adamu Aliero, Adams Oshiomole, Ibrahim Gaidam, Seriake Dickson, Ibrahim Dankwambo, Aliyu Wammako da Gbenga Daniel.
A cikin karar, SERAP ta bayyana cewa sashe na bakwai na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka gyara) ya bukaci tsofaffin gwamnoni da su daina karɓar albashi tare da fansho da kuma mayar da duk wani kuɗaɗen fansho da suka karɓa.

