Gwamnatin Najeriya Za Ta Binciki Yadda Buhari Ya Tafiyar Da Shirin N-Power
Gwamnatin ta kuma ce ta dakatar da shirin gaba daya
Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnatin Tarayya ta sanar da dakatar da shirin N-Power har sai abin da hali ya yi.
Ministar Jinkai da Yaki da Talauci, Betta Edu ce ta sanar da daukar matakin a cikin tattaunawarta da gidan talabijin na TVC a ranar Asabar.
Ta ce sun yanke shawarar daukar matakin ne sakamakon gano wasu kura-kurai da suka yi a cikinsa.
Ministar ta kuma ce tuni gwamnatinsu ta kaddamar da bincike kan yadda aka kashe kudade a cikin shirin tun a lokacin da aka kirkire shi.
Ta kuma ce yanzu haka, akwai wasu daga cikin wadanda ke cin gajiyar shirin, amma sam ba sa zuwa wuraren ayyukansu.
Betta Edu ta ce wasu daga cikin irin wadannan mutanen ya kamata a ce sun fita daga cikin shirin tun a shekara ta 2022, amma har yanzu ana ci gaba da biyansu albashi.
Ta ce, “Akwai abubuwa da dama da suke tafiya ba daidai ba. Akwai lokutan da muke tuntubar makarantun da suke aiki, amma ba sa nan. Ba sa aiki amma suna ikirarin suna bin mu bashin albashin wata takwas ko tara.


