Home Labarai Da sana’ar sayar da soson wanka mu ke samun rufin asiri a Ogun – Alhaji Ya’u

Da sana’ar sayar da soson wanka mu ke samun rufin asiri a Ogun – Alhaji Ya’u

by Muhsin Tasiu Yau

Daga DAUDA USMAN a Legas

Wani ɗan kasuwa mai gudanar da harkokin kasuwancin sayar da sosan wanka wanda ake kiransa da suna Kakan a Jihar Ogun, Alhaji Ya’u Samaila, ya bayyna cewa, da wannan sana’ar su ke samun rufin asiri a Ogun.

Alhaji Ya’u, wanda ya kasance ɗan asalin ƙaramar hukumar Samaila ne da ke cikin Jihar Kano mazaunin Ogun, kuma shugaban Ƙungiyar Masu Sana’ar Kasuwancin Sosan Wanka Kakan a garin Ibafo ta Ogun ya bayyana cewa, shi da sauran ‘yan Kasuwa masu sana’ar kasuwancin sosan kakan a garin Ibafo su na ƙara samun nasarori a wajen gudanar da harkokin kasuwancin su na kakan a kowanne lokaci a Ogun da kewayenta gabaɗaya.

Shugaban ƙungiyar a garin Ibafo Alhaji Ya’u Sumaila ya yi wannan tsokaci ne a ofis ɗin ƙungiyar ta su da ke garin Ibafo jim kaɗan bayan kammala taron su da waɗansu daga cikin ƙusoshin ƙungiyar wanda su ka saba yi aduk bayan ƙarshen mako domin tattaunawa bisa kan abubuwan da za su kawo cigaba tare da daƙile matsalolin da ƙungiyar ta ke fuskanta gabaɗaya.

Ya bayyana wa wakilin jaridar Blueprint Manhaja a garin Ibafo gaskiyar wannan al’amari, inda shugaban ƙungiyar ya cigaba da cewa, haƙiƙa shi da sauran ‘yan kasuwa masu sana’ar kakan a garin Ibafo a halin yanzu suna cike da farin ciki tare da godiyar Allah, a cewarsa, domin kuwa a halin yanzu Allah Ubangiji ya sanya wa sana’ar su albarka da kuma rufin asiri ta ɓangaren kasuwancin su na kakan.

Ya ƙara da cewa, tun da su na ci, su na sha tare da tufatar da iyalan su da sauran al’amuran su na yau da kullum ba tare da wata matsala ba, ya ce, a kan hakan yake ƙara shawartar ‘yan ƙungiyarsa ta masu kasuwancin kakan a farin Ibafo dama jihar Ogun bakiɗaya da su cigaba da riqe sana’ar su ta kakan hannu bibiyu domin samun hawa tudumun-tsira.

Ya ci gaba da jawo hankulan ‘yan ƙungiyar da su cigaba da zaman lafiya da sauran ƙabilun garin Ibafo dama na Jihar Ogun bakiɗaya.

Sannan kuma ya ce, yana mai jinjina wa Sarkin al’ummar Hausawan garin Ibafo, Alhaji Shehu Usman Dan Yaro Ibafo, inji shi bi sa ƙoƙarin sa na haɗa kawunan al’ummar Hausawa da na sauran ƙabilun garin Ibafo domin su cigaba da zaman Lafiya bakiɗaya.

Related Posts

Leave a Comment