Home Labarai TSARODan Majalisar Tarayya, Abdullahi Balarabe, Ya Bukaci A Ba Mutane Damar Kare Kansu

TSARODan Majalisar Tarayya, Abdullahi Balarabe, Ya Bukaci A Ba Mutane Damar Kare Kansu

by Muhsin Tasiu Yau

Ɗan majalisa mai wakiltar Bakori da Danja a zauren Majalisar Wakilai, Abdullahi Balarabe Dabai, ya buƙaci a bai wa al’ummar yankin damar kare kawunansu daga hare-haren ‘yan ta’adda.

Honorabul Abdullahi Dabai ya roƙi a ɗauki matakin bai wa kowa damar kare kansa ta hanyar kulawa da sa idon jami’an tsaron Najeriya.

Ya bayyana hakan ne a zauren majalisar, a zaman da ta yi na ranar Talata, 03 ga watan Oktoba kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

An buƙaci a ajiye sojojin a yankin da matsalar tsaro ta yi ƙamari

Abdullahi Dabai ya kuma buƙaci a kai barikin soji a mazaɓarsa ta Bakori-Danja da ke jihar Katsina, wacce take fama da yawaitar hare-haren ‘yan bindiga.

Ya kuma bukaci a ajiye sojojin a wasu yankuna na mazaɓar ta sa da suka fi fuskantar hare-haren masu garkuwa da mutane a cikin ‘yan kwanakin nan.

A jawabin da ya gabatar yayin miƙa kudirin na haɗin guiwa, Ɗan majalisar ya ce:

“Ina alfaharin miƙa kudirin kafa ‘yan sandan yanki ta yadda mutane zasu samu damar ɗaukar makami su kare kansu ta hanyar kulawar jami’an tsaro.”

“Haka kuma ina roƙon a girke dakarun sojoji a Guga, Kakumi da Kandarawa da ke ƙaramar hukumar Bakori da kuma kafa sansanin sojoji a mazaɓar Bakori da Ɗanja.”

Ƙudurin da ya gabatar ya samu karɓuwa a gaban majalisar, inda ya ba da tabbacin cewa za a yi duk abinda ya dace wajen tabbatar da samuwar tsaro a yankin da ma ƙasar baki ɗaya.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar Najeriya musamman ma dai na yankin Arewacin Najeriya ke ƙara kokawa kan ƙaruwar hare-haren yan bindiga a yankunansu.

Related Posts

Leave a Comment