Girgizar kasa ta kashe fiye da mutum 2000 a Afghanistan.
Hukumar kula da yanayi ta Afghanistan ta tabbatar da cewa girgizar kasar, mai karfin maki 6.3 da ta auka wa kasar ranar Asabar, ta kashe mutum 2,053 kawo yanzu. Kazalika ta lalata sama da gida 1,300.