2k
A baya kotun sauraren ƙararrakin zaɓe ta yi hukuncin soke nasarar sa sakamakon ƙarar da jamiyyar APC ta shigar tana mai ƙalubalantar nasarar dan takarar NNPP da zargin sa da gabatar da takardun firamare na bogi.
Kotun ɗaukaka ƙarar a hukuncin ta na yau ta tabbatar wa da Mukhtar Umar Yarima nasara, tare da warware hukuncin da kotun saurarar ƙararrakin zabe tayi na sanya Hafizu kawu na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

