Home Labarai An Samu Masu Juna Biyu Da Kanjamau A Masu Neman Auran Gata A Kano — Hisba

An Samu Masu Juna Biyu Da Kanjamau A Masu Neman Auran Gata A Kano — Hisba

An Samu Masu Juna Biyu Da Kanjamau A Masu Neman Auran Gata A Kano — Hisba

by Muhsin Tasiu Yau

An Samu Masu Juna Biyu da Kanjamau a Masu Neman Auran Gata a Kano — Hisba

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce an samu wasu da ke dauke da cututtuka a cikin wadanda ke neman ayi masu auren gata.

Jaridar Vanguard ta ce cututtukan da aka samu sun hada ciwon hanta na Hepatitis B, sikila da kanjamu.

Mai magana da yawun bakin hukumar ta Hisbah, Lawan Fagge ya ce an gano wannan ne a wajen gwaje-gwajen da ake yi kafin auren.

Har ila yau akwai matan da aka samu su na dauke da juna biyu a yanzu haka. A musulunci, ba a yin aure dauke da ciki har sai an yi tsarki.

Malam Lawan Fagge ya ce tuni an maye guraben irin wadannan mutane da aka samu da wasu dabam domin su ci moriyar tsarin gwamnatin.

Hukumar Hisbah za ta taimakawa masu dauke da cututtukan da maganguna, kuma ana basu shawarwarin ganin yadda za su samu lafiya.

Related Posts

Leave a Comment