Home Labarai Gwarzuwar Nijeriya Madam Felicia Adebola Adeyoyin

Gwarzuwar Nijeriya Madam Felicia Adebola Adeyoyin

by masta


Wannan ita ce FELICIA ADEBOLA ADEYOYIN matar da ta rubuta taken Alwashin Kasa wato National Pledge da ake karantawa duk bayan take Najeriya.

Malama Filicia ta rubuta taken ne a shekarar 1976 bayan da yaranta da suka dandana romon taken alwashin a kasashen da ta zauna irinsu Amurka da Ghana suka addabe ta da tambayar yaya aka yi Najeriya ba ta da wannan garabasa? Hakan ta sa ta dauki biro na wancan zamanin ta rubuta taken a matsayin ‘yar makalar da ba ta san inda zata kai ta ba. Inda ta mika wa jaridar Daily times, ita kuma Jaridar ta buga a wata fitowarta a watan Yuli 1976 har aka wa taken lakabi da Loyalty to the Nation, Pledge. Caraf wannan jarida ta shiga hannun abokin dasawar Shugaba Obasanjo Emmanuel Adewusi, Shi kuwa ya nuna wa shugaban kasar na wancan lokacin, ai ko da karantawa sai Shugaba Obasanjo ya gamsu, ya kuma kafa kwamitin da suka tantance suka amince da wannan Alwashi suka yanke shawarar kaddamar da shi a ranar 6 ga Satumba, 1976, wato lokacin ƙaddamar da Ilimin Firamare Kyauta na Duniya (UPE). Hakan ko aka yi aka gabatar da wannan Take manne da taken wanda mutane za su karanta don haɓaka kishin ƙasa, aminci, kyawawan dabi’u da ra’ayin hidima ga uwa Najeriya
Madam Felicia wadda yar asalin jahar Oyo ce kuma yar gidan Sarautar Shaki, kuma malamar makarantu ta mutu a watan Mayun shekarar 2021.

Felicia wata abar koyi ce a fannin dabarun hidimta wa kasa domin ta bar tata gudunmuwar wajen dora kowane dan kasa mai karanta wannan alwashin a wata turba ta alkawarin hidimta wa kasarsa tare da bar wa Allah sauran lamarin a karshen alwashin ( So help me God) irin hidimar da ba za a manta da ita ba ko da kuwa ba ta bayar da abinci da man fetur ba ce

Related Posts

Leave a Comment