Home Labarai Amfanin Kabewa a jikin Dan’adam

Amfanin Kabewa a jikin Dan’adam

by masta

Zuwa ga Iyali
Daga
Bilkisu Yusuf Ali

Kabewa dan itace ce kuma mai saukiin samu da saukin sarrafawa mai matukar amfani a jikin al’umma don tana taimakawa sannan kuma ba ta da tsada . Sannan kabewa tana da wata fa’ida ta musamman wadda ana iya samunta a kowanne lokaci wato damina da rani. Kabewa tana dauke da sinadaran da jikin dan’adam ke buKaya. A wani bincike da manazarta suka yi an nuna cewa kabewa tana dauke da sinadarai na protein da carbohydrate da fiber da vitamin A da Vitamin c da Vitamin B2 da Vitamin E da kuma Iron. Daga cikin amfaninta da kuma yadda ake sarrafa ta akwai:

Ana samun kabewa a yayyankata a sami dabino mai dan dama a daka shi ya yi laushi a dafa su sannan a tace ruwanta kofi daya a sha da madara ko nono mai kyau a sha kwana uku a jere ko kwana 7 yana dawo da ni’imar mace ko da ba tad a ni’ima.

Kabewa tana inganta lafiyar zuciya. Kabewa na inganta lafiyar zuciya ta hana ta kamuwa da wasu cutuka.

Kabewa Tana kara lafiya da karfin gani tana magance raunin ido.

Kabewa tana magance larurorin fata. Ana samun kabewa a hada da danyen kwai da zuma da leman tsami da dan kurkum kadan a shafe jiki da shi a bar shi har zuwa tsahon minti 30 sannan a sa ruwan dimi a wanke jiki da shi. A maimaita kwana 3-7 za a ga yadda jiki zai yi kyau da santsi.

Kabewa tana magani da kariya daga cutar jeji musamman in aka dimanci cinta akai –akai.

Ga namijin da yake fama da karancin sinadari na maniyyi ko rashin karfin gaba a samu kabewa a dafata da citta da tafarnuwa da farar albasa Ana iya Kara zuma in sha Allahu za a dace.

Maganin gajiya . Kabewa tana magance gajiya yayin wasu aikace-aikace na yau da kullum.

Ga mai dan jiki da saurin jin ciwo yawan amfani da kabewa yana da matukaar amfani da Fa’ida.

Ga mai karancin jini musamman masu larurar karancin jini ko jininsu ya yi kasa Ana dafa kabewa a ci in son samu ne kullum a kalla kwana 7 a jere in sha Allah za a dace.

Ga mai Neman Karin bayani ko kuma wata matsala ama iya tuntubar wannan lambar don samun Karin bayani 08054137080

Related Posts

Leave a Comment