A cikin kokarin Gwamnatin Jihar Katsina na kawo karshen matsalar tsaron da ya addabi wasu sassan Jihar.
Kwamishinan ma’aikatar kula da tsaron cikin gidan gami da harkokin cikin gida Hon. Nasiru Mu’azu Danmusa.
Ya gana da masu ruwa da tsaki na kananan hukumomin da sukafi fama da matsalar tsaro a Jihar ranar alhamis 23/8/2023.
Masu ruwa da tsakin kananan hukumomin da kwamishinan ya gana dasu sun hada dana Sabuwa, Dandume, Faskari, Funtua, Kankara, Batsari, Jibia, Danmusa, da Safana.
Manufar ganawar domin bayyana ma masu ruwa da tsakin tsare, tsare akan kokarin Gwam natin Jihar Katsina na kawo karshen matsalar tsaro a Jihar.
Masu ruwa da tsakin sune yan majalisar dokoki masu wakiltar kananan hukumomin, shugaban nin kananan hukumomin, Hakimmai, Jami’an tsaro da Limamai.
Taron ganawar masu ruwa da tsaki akan tsaro da aka gudanar a ma’aikatar tsaron cikin gidan ya samu halartar kwamishinan yan Sanda na Jihar Cp. Aliyu Abubakar Musa.
Sai mai baiwa Gwamna shawara akan kula da tsaron Al’umma, babban Sakataren ma’aikatar, da Daraktocin Ma’aikatar.


